Ilimi gameda tekun pacific ocean



YAKAMATA KASAN WANI ABU GAMEDA WANNAN.

1. Shekaru kamar dari biyar dasuka wuce, wani mutum dan kasar spain mai suna Vasco Nunez de Balboa shine mutum na farko wanda yafara yin nazari gameda tekun pacifin ocean daga yammacin amurka.

2. Lafazin kalmar pecific yana nufin peaceful a turance, Pacific ocean yasamo wannan suna ne daga wani mutum mai suna ferdinard magellan, ya sanya masa suna ne da "mar pacific" wanda hakan yana nufin peaceful sea a turance.

3. Tekun pacific yana nan a tsakanin america da Asia dakuma Austrian continent zuwa yammacin duniya. Wanda ahalin da ake ciki shi wannan tekun pacific masana sun rabashi gida biyu wato akwai north pacific ocean dakuma south pacific oceans.

4. Tekun pacific ocean shine teku mafi girma a duniya domin yafi surface na earth fadi dakuma girma sosai nesa ba kusa ba koda kuwa za'a hada girman continent na damuke dasu a duniya bazasu taba kai tekun pacific girma ba.

5. Tekun pacific yanada zurfi ainin sosai , wanda ahakan kuma yanada hanyoyi acikin sa dakuma kwazazzabo duk a karkashin sa kamar yadda masu bincike na kungiyar HMS challengers suka gano a shekarar alif 1875.

6. Akwai rijiyoyin wuta na volcanoes acikin tekun pacific ocean wanda suke kewaye da tekun. Hakan yasa nan tekun yazama kamar wani waje ne na faruwan ambaliyar ruwa sakamakon girgizan kasa dayake yawan faruwa acikin sa saboda motsin da tactinic plates suke yi akarkashin kasan wajen, bincike yagano cewa akwai akwai rijiyoyin wuta na volcanoes acikin tekun pacific ocean wanda yawan su yakai 75,000.

7. Tekun pacific shine teku wanda yake dauke da island wato tsibiri tsibiri kala kala wanda adadin yawan su yakai dubu 25,000. Domin akwai wanda wasu tsibirin ma akwai garuruwan da mutane suke rayuwa akansu.

8. Tekun pacific yana kara girma duk shekara da girman inchi daya wato one inches a turance sakamakon motsin da tactonic plates keyi acikin tekun pacific kamar yadda bincike ya nuna .

9. Haka zalika tekun atlantic ocean shima yana kara girma da inchi daya duk shekara kamar yadda bincike yagano.
Tekun pacific ocean dakuma tekun atlantic oceans wanda sune teku mafi girma a duniya sun hadu da junan su ayankin northern america ta wajen Alaska .

10. Wannan haduwar yasanya sun zama abin al'ajabi ga mutanen duniya sakamakon gasudai sunzo kusa dajuna amma kuma basu gauraya da juna ba wato kowanne na cin gashin kansa.

11. Ubangiji Allah ta'ala shiyayi wannan iko nasa kamar yadda Ya bada labari wa Annabi Muhammad (s.a.w) shekaru 1400 dasuka wuce, acikin suratul - Ar-rahman ayata 19 zuwa na 20 Allah yayi magana akan pecific ocean dakuma atlantic ocean.

12. Idan mai karatu ya kalli hoton dana daura zaiga hoton tekun guda biyo kuma kowanne da kalarsa. Daya daga cikin su fresh water ne daya kuma salty water ne wato akwai gishiri acikinsa.

13. Tekun pacific shine teku wanda yake fresh water ne wato bayada gishiri acikinsa sosai , shi kuma tekun atlantic ocean yanada gishiri sosai wato salty ne.

Wannan shine karshen karatun mu gameda tekun pacific ocean.

Post a Comment

0 Comments