YAKAMATA KASAN DA WANNAN GAMEDA AZURFA
1. Azurfa shine karfe mafi sheqi Kuma mafi daukan haske wato reflection a turance Wanda fiyeda zinare.
Wani zaice lu'u lu'u (diamond) yafi shi, karka manta lu'u lu'u non metal ne (ba karfe bane) domin karfe shine abinda yake iya karban wutan lantarki yabi ta jikinsa a bokon ce.
Wanda shi lu'u lu'u (diamond) baya karban wutan lantarki kwata kwata.
2. Kasar Mexico, USA, Canada, Russia da Kuma Australia sune kasashen da sukafi Samar wa duniya karfen azurfa.
Ma'ana dai sune kasashen da sukafi arzikin karfen azurfa, Amma Kuma kasar Mexico itace kan gaba.
3. Karfen azurfa Yana daga cikin karfe mafi karfi wajen karban wutan lantarki shiyasa darajar sa yakara karuwa a duniya.
Domin kafin karfen azurfa ya narke saiya Sami zafin (temperature) da yakai 900 degree celcius.
A glass na bayan motoci, zakaga wasu Zanen layuka hakannan , wannan layukan da kake gani karfen azurfa ne.
4. Karfen azurfa ana samunsa natural ne domin ba'a iyayin sa artificial kamar yadda ake iyayin lu'u lu'u artificial.
Ma'ana dai karfen azurfa ana samunsa ne natural Kuma baya bukatan wasu gyare gyare (processing).
5. Karfen azurfa da zinare sune karfen da Allah yayi su a matsayin kudi Wanda za'a na amfani dashi wajen cinikaiya a muslunci.
Wannan yasa tin farkon duniya zinare da azurfa suke da matukar daraja na gaske.
Darajan zinare da azurfa (silver) baya tabayin baya saidai ma yahaura sama.
Wannan yasa dayawan mutane suke fuskantan wasu abubuwa kamar na tsafi gameda lamarin azurfa.
5. Mutane sun yi imanin cewa idan ka kuskura kashiga cikin ruwa (Rafi ko dam ko tafki) alhali zoben azurfa Yana hannunka to zaka nemi wannan zoben azurfan karasa.
Zai fice daga hannun ka batareda kasan lokacin da yafita ba.
Ko wanki kakeyi da zoben asurfa zaka iya neman sa karasa shi domin yanada wani boyayyen lamari tsakanin sa da ruwa Wanda Allah ne yafi kowa sanin lamarin.
6. Ana amfani da azurfa da sinadarin iodine (ayodin) wajen Samar da ruwan sama wato artificial rain aturance.
Kasashen dasuka ci gaba irinsu America, Dubai da Kuma China suna amfani da azurfa (silver iodide) wajen Samar da ruwan sama a duk sa'ilin da suke so bisa yadda na Allah ta'ala.
Shiyasa wasu ke kallon silver yanada wani Abu tattare dashi kamar na tsafi(magical behavior).
7. Haka zalika kasashen amurka suna amfani da chokalin silver (silver spoon) wajen bawa yaransu abinci domin sunada fahimtan cewa yaran da suke cin abinci a chokalin silver sunfi lafiya.
Kamar yadda Suma kasar China suna sanyawa yaran su zoben azurfa domin sunada fahimtan cewa Yana taimakawa wajen Kare yara kanana daga wasu sharri.
8. A kasashen mu na yammacin africa, dayawan mutane sunada fahimtan cewa matukar bakada lafiya zazzabi ko wani rashin lafiya yakamaka alhali ahannun ka akwai zoben azurfa (pure silver) ba jabu ba to zoben azurfan zakaga ya canza kala shi da kansa.
Wasu da Haka suke gane cewa basuda lafiya.
9. Haka zalika dayawan mutanen Africa, sunada fahimtan cewa matukar akwai zoben azurfa ahannun ka to zaiyi wahala sihiri (magic) yakama ka.
Hassalima idan kanada zoben azurfa ahannun ka saikaga alamun ya tsage (broken) hakannan to bisa alamu anso ayi maka sihiri ko jifa.
Wani ma idan yakwanta bacci akwai zoben azurfa ahannun sa, idan akayi masa jifa to zoben azurfan zai fita daga hannun sa.
Saidai kaga zoben azurfan agefen ka yafita, zaka rasa ya akayi yafita.
Zandakata anan Haka, Allah shine Mafi sani.
0 Comments